ABNA24 : Taron wanda ke samun halartar wakilai daga kasashen Amurka, China, Qatar, Biritaniya, Uzbekistan, Pakistan da na MDD da na kungiyar tarayyar turai, na mai bukakar kungiyar Taliban ta dakatar da matsa kaimin da ta ke ta kuma shiga tattaunawa domin cimma yarjejeniyar siyasa.
Saidia an bayyana cewa akwai wuya taron ya haifar da da mai ido, duba da halin da ake ciki a kasar ta Afganistan a daidai lokacin da kungiyar ta Taliban ke ci gaba da dannawa kan wasu yankunan kasar.
Yarjejeniyar zaman lafiya dake tsakanin gwamnatin Kaboul da Taliban da kuma Amurka a daya bangare wacce aka buda a watan Satumban bara ta tanadi janye gabadayan dakarun kasa da kasa kafin nan da ranar 31 ga watan Augusta 2021.
Saidai duba da yadda yarjejeniyar ta shiga rashin tabbas, kungiyar Taliban ta kaddamar da farmaki a watan Mayu a daidai lokacin da Amurka ta fara janye dakarunta.
Kazamin fadan da ake gwabzawa tsakanin Taliban da dakarun gwamnatin Kaboul, ya tilasta wa ‘yan kasar sama da 240,000 yin gudun hijira tun daga farkon watan Mayu da ya gabata.
342/